logo

HAUSA

Sin da Amurka sun gudanar da sabon zagayen tattaunawa game da tsara manufofin waje

2024-02-29 20:02:14 CMG Hausa

Wakilai daga tsagin Sin da na Amurka, sun gudanar da sabon zagayen tattaunawa game da tsara manufofin waje, a rana 27 ga wata a birnin Shanghai.

A cewar ma’aikatar wajen Sin, jami’an da suka shiga tattaunawar sun hada da mataimakin ministan waje, kuma babban daraktan sashen tsara manufofin waje Miao Deyu, da daraktan ma’aikata a ofishin sakataren tsara manufofi na ma’aikatar wajen Amurka Salman Ahmed.

Sassan biyu sun zurfafa tattaunawa mai gamsarwa, game da manufofin harkokin wajen kasashen su, da batutuwan dake jan hankalin kasashen a shiyyoyi da sassan kasa da kasa.   (Saminu Alhassan)