logo

HAUSA

An bude babban taron duniya karo na 7 a kan batun makamashi a birnin Abuja dake tarayyar Najeriya

2024-02-29 10:25:59 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci da a hada kai domin tattaunawa a kan hanyoyin da za su kawo karshen kalubalen makamashi da kasar ke fuskanta.

Ya bukaci hakan ne a birnin Abuja yayin da yake bude babban taron duniya karo na 7 a kan batun makamashi, inda ya yi fatan cewa batun janye tallafin man fetur yana daya daga cikin mahimman batutuwan da taron da za a kammala ranar 1 ga watan gobe zai tattauna a kai.

Daga tarayyar Najeriya Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya samu wakilcin ministan yada labarai Alhaji Muhammad Idris, ya ce, wadatuwar makamashi shi ne abu mafi mahimmanci ga ci gaban kowacce kasa a duniya, inda ya kara tabbatar da cewa, duniya na kan ganiyar karni na 21, a don haka ya zama wajibi Najeriya ta sake nazarin manufofinta a kan makamashi domin tabbatar da kyakkyawar makoma ga kowa.

Shugaban Tinubu ya ci gaba da bayanin cewa, tallafin man fetur da kasar ta jima tana aiwatarwa ya haifar da nakasu mai yawa ga albarkatun tattalin arzikin kasa, lamarin da ya sanya gwamnati gaza sakewa sosai wajen zuba jari a mahimman bangarorin da suke da alaka da makamashi.

Har ila yau ya ce, a bayyane take akwai alaka tsakanin batun samar da makamashi da kuma yanayin tsaro a kasa, kasancewar yanzu haka yawan tashe-tashen hankula da kasashen duniya ke fuskanta suna da nasaba ne da makamashin da ake samu a yankuna, a sabo da haka kamar yadda ya fada, gwamnati tana bakin kokarinta wajen samar da yanayin mai kyau ga masu zuba jari a bangaren makamashi da sauran bangarorin na tattalin arziki.

A nasa jawabin sakatare-janaral na kungiyar kasashen masu arzikin mai na duniya OPEC Haithan Al-Ghais cewa ya yi, “Abun da ake nema a wajen manyan kasashe masu samar da mai kamar Najeriya da sauran kasashen Afrika dama na sauran nahiyoyi shi ne su kawo daidaito da kwanciyar hankalin da ake bukata a kasuwar hada-hadar mai, ta yadda masu zuba jari za su sami kyakkyawan yanayi wajen saka jarinsu.” (Garba Abdullahi Bagwai)