logo

HAUSA

Za a yi gasar kokowar gargajiya a birnin Zinder na Nijar

2024-02-29 11:02:35 CMG Hausa

Birnin Zinder zai karbi bakuncin gasar kokowar gargajiya daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Maris mai zuwa da ta samu halartar yankunan Nijar guda 8.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Wannan gasar motsa jiki za ta dauki taken “gasar ceton kasa” da kuma za ta gudana tare da cin kofin shugaban CNSP, shugaban kasa birgadiye-janar Abdrourahamane Tiani.

Gwamnan yankin Zinder, kanal Issoufou Labo tare da rakiyar wata tawagar kungiyar kokowar gargajiya ta kasa FENILUTTE ya kai ziyara gani da ido a ranar Talata da ta gabata a filin wasan kokowar gargajiya na Langa Langa dake birnin Zinder cikin tsarin shirye-shiryen wannan babbar haduwa domin baki da za su ziyarci yankin Zinder, su samu zarafi mai kyau na walwala da jin dadi tare da dukkan tawagogin da za su zo ta yadda ’yan kasa da ma duniya za su karda wannan kwanbala, in ji gwammnan Zinder.

Hukumomin yankin Zinder da kungiyar kokowar gargajiya ta FENILUTTE sun dauki niyyar domin ba da wani sabon lumfashi ga filin wasan kokowa ta yadda zai amsa sharudan da ake bukata, a cewar gwamna Issoufou Labo, tare da kuma bayyana gamsuwarsa bisa zabin da aka yi wa birnin Zinder domin karbar bakuncin wannan babban taro.

Kokowar gargajiya ita ce wasan motsa jiki mafi karbuwa a wajen al’ummar Nijar, kuma gasar cin takobi karo na 44 ta gudana daga ranar 22 zuwa 31 ga watan Disamban shekakar 2023 a yankin Agadez tare da nasarar dan kokowar yankin Dosso Issaka Issaka.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyar Nijar.