logo

HAUSA

Kasar Chadi za ta gudanar da zaben shugaban kasa a watan Mayu

2024-02-29 10:43:40 CMG Hausa

Hukumar zabe ta kasar Chadi ANGE ta sanar a ranar Talata cewa, kasar Chadi za ta gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko a ranar 6 ga watan Mayu, inda za ta karbi sunayen ‘yan takarar da aka tsayar daga ranar 6 zuwa 15 ga Maris.

A ranar 26 ga watan Maris ne za a fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe yayin da za a gudanar da yakin neman zabe daga ranar 14 ga watan Afrilu zuwa 4 ga Mayu, kamar yadda shugaban ANGE Ahmed Bartichet ya shaidawa manema labarai a N'Djamena, babban birnin kasar.

Bartichet ya kara da cewa, a ranar 22 ga watan Yuni ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben idan har ba a samu cikakken wanda ya yi nasara ba a zagayen farko.

Shirya gudanar da zaben shugaban kasar zai yi nuni da komawa kan tsarin mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka, wanda ta kada kuri'ar raba gardama a watan Disambar bara, a cewarsa. (Yahaya)