logo

HAUSA

Sin har kullum na raba makomarta ta bai daya da kasashe masu tasowa

2024-02-29 19:06:32 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce a matsayin ta na kasa mai tasowa, Sin ta shiga rukunin kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasa, don haka har kullum take raba makomarta ta bai daya da sauran kasashe masu tasowa, tana kuma nacewa manufar kare moriyarsu ta bai daya.

Mao Ning ta bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin da take jagorantar taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa. Ta yi tsokacin ne lokacin da aka yi mata tambaya mai nasaba da hakan.

Game da rikicin Gaza kuwa, jami’ar ta ce ya zama wajibi sassan kasa da kasa su gaggauta aiwatar da matakai, tare da dora dukkanin muhimmanci ga ingiza bukatar dakatar da bude wuta, da kawo karshen yaki, tare da kare lafiyar fararen hula.

Har ila yau, Mao Ning ta ce Sin na da imanin cewa tsawaitar tashin hankali dake gudana a Ukraine, ba zai haifar da ‘da mai ido ga al’ummun kasa da kasa ba. Don haka aikin dake gaban wakilan musamman na Sin a harkokin Turai da Asiya dake zirga zirga tsakanin kasashe daban daban, shi ne cimma daidaiton kawo karshen yaki.

Don gane da zargin wai "Sin na sayen muhimman bayanai daga wasu Amurkawa" kuwa, Mao Ning ta ce ya kamata Amurka ta dakatar da shafawa Sin bakin fenti.

Sai kuma batun tekun kudancin Sin, wanda jami’ar ta ce kamata ya yi kasashen dake da ruwa da tsaki a batun su kauracewa shiga duk wani hadin gwiwar tsaro, da ka iya gurgunta moriyar sauran kasashen yankin, ko jefa yanayin zaman lafiyar yankin cikin hadari. (Saminu Alhassan)