logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da shugabannin dake kula da gyara tsarin kwamitin sulhu na MDD karo na 78

2024-02-29 10:25:23 CMG Hausa

Ministan wajen Sin Wang Yi ya gana da shugabannin dake kula da batun gyara tsarin tattaunawa tsakanin gwamnatoci, na kwamitin sulhu na MDD karo na 78, wato zaunannen wakilin Kuwait a majalisar, Tareq M. A. M. Albanai, da kuma zaunannen wakilin Austria Alexander Marschik.

Wang Yi ya bayyana cewa, bangaren Sin na goyon bayan shugabannin biyu wajen inganta gyare-gyare a kwamitin sulhu ta madaidaiciyar hanya cikin kwanciyar hankali, da kara wakilci da ikon jin muryoyin kasashe masu tasowa, ta yadda kananan kasashe za su samu damar shiga ayyukan yanke shawara, kuma dukkan mambobi kasashe za su ci moriyar kwaskwarimar. 

Ya kara da cewa, ya kamata a dauki batun kiyaye hadin gwiwar al’ummar kasa da kasa da muhimmanci, da tsayawa tsayin daka kan tattaunawa tsakanin gwamnatoci, da jagorantar kasashe mambobi wajen gudanar da tattaunawa, da kuma neman samun matsaya guda daya da kasa da kasa suka cimma.

A nasu bangare, Albanai da Marschik sun yabawa kasar Sin, inda suka ce, ta dade tana himmantuwa wajen karfafa aikin MDD da kare ra’ayin bangarori daban daban, da kuma kare ka’idojin tsarin dokokin MDD. Sun kara da cewa, suna fatan ci gaba da mu’amala da tattaunawa da kasashe mambobi, ciki har da bangaren Sin, game da batun aiwatar da gyare-gyare a kwamitin sulhun. (Safiyah Ma)