logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya gana da takwaransa na Saliyo

2024-02-28 19:53:29 CMG Hausa

Da yammacin Larabar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da takwaransa na Saliyo Julius Maada Bio, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin.

Yayin zantawar shugabannin biyu a birnin Beijing, shugaba Xi ya ce kasar sa da Saliyo na da dadadden tarihin kawance, kuma Sin na goyon bayan al’ummar Saliyo wajen zabar hanyar ci gaba daidai da yanayin kasar su. Ya ce Sinawa da al’ummun kasashen Afirka na da makomar bai daya. Kaza lika, har kullum Sin na daukar bunkasar dunkulewa da hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka, a matsayin muhimmin jigo cikin manufofin ta na waje, kuma za ta kara dunkule ci gaban ta da na nahiyar Afirka, da ma duniya baki daya.

A nasa bangare, shugaba Bio ya ce Sin aminiya ce da Saliyo ke iya dogaro da ita, kuma ta shirya karfafa tsare tsare, da hadin gwiwa da Sin a harkokin yankin da take, da ma na sauran sassan kasa da kasa.

Bayan ganawar, shugabannin biyu sun ganewa idanun su sanya hannu kan takardun bunkasa hadin gwiwar kasashen su. Kaza lika sassan biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa, ta zurfafa cikakkiyar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Saliyo.  

Kana firayin ministan kasar Li Qiang shi ma ya gana da shugaba Bio a Yau Laraba. (Saminu Alhassan)