logo

HAUSA

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta sanar da dakatar da zanga-zanga a kasar

2024-02-28 10:57:42 CMG Hausa

Kungiyar ’yan kwadago ta Najeriya wato NLC ta sanar a daren jiya Talata cewa, ta dakatar da yin zanga-zanga na tsawon kwanaki 2, wanda a baya aka yanke shawarar gudanarwa.

Bisa sanarwar da NLC ta bayar, an ce, zanga-zangar ta riga ta cimma makasudin da aka yi hasashe, wato ana bukatar gwamnatin Najeriya ta tabbatar da aiwatar da bukatun da kungiyar ta gabatar a watan Oktoban shekarar bara cikin kwanaki 14 mai zuwa, daga ciki akwai batun kara albashi mafi karanci da sauransu.

Har ila yau a jiya, karamin ministan kula da harkokin kwadago da guraben aikin yi na kasar, Nkeiruka Onyejocha, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya ta riga ta kammala kusan 90% na batutuwan dake cikin yarjejeniyar da ta sa hannu da kungiyar NLC a watan Oktoba na shekarar bara. Amma shugaban kungiyar ’yan kwadagon Joe Ajaero ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka gudanar da zanga-zanga na wannan karo shi ne rashin gamsuwa da hauhawar farashin abinci, ba bukatar duba mafi karancin albashi kadai ba. (Safiyah Ma)