logo

HAUSA

Babban bankin Nijeriya ya kara kudin ruwa zuwa kaso 22.75

2024-02-28 11:36:44 CMG Hausa

Babban bankin Nijeriya ya dauki matakin kara kudin ruwa da maki 400 zuwa kaso 22.75.

Gwamnan babban bankin Nijeriya, Yemi Cardoso, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kula da manufofin kudi na kasar, ya bayyanawa manema labarai bayan kammala wani taro cewa, matakin wani muhimmin yunkuri ne ga manufar kudi ta kasar, wanda ke da nufin mayar da martani ga karuwar farashin kayayyaki da rashin daidaito a kasuwar musayar kudaden waje.

Da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Ademidun McCann, wani masanin tattalin arziki mazaunin birnin Abuja, ya ce matakin na da nufin tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki da karfafa gwiwar masu zuba jari yayin da ake fama da rashin tabbas game da ci gaban tattalin arziki.

Ademidun McCann ya kara da cewa, yayin da matakin kara kudin ruwa ka iya taimakawa rage hauhawar farashi, tsadar karbar rance ka iya rage sayayya da harkokin zuba jari, wanda ka iya kara matsi ga ci gaban tattalin arzikin kasar. (Fa’iza Mustapha)