logo

HAUSA

Jami’an tsaro na hadin gwiwa na jihar Boboye sun kama abubuwa masu fashewa guda 1980

2024-02-27 13:57:30 CMG Hausa

Jami’an tsaro na hadin gwiwa na jihar Boboye, yankin Dosso, dake bisa umurnin kwamandan jami’an tsaro na masu koren hulla Harouna Dalimane sun kama abubuwa masu fashewa a ranar Lahadi 25 zuwa ranar Litinin 26 ga watan Fabrairun shekarar 2024 a kauyen Fabidji. 

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu, Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Da misalin karfe 6 ne na ranar Litinin da yamma, jami’an tsaron FDS suka kama wasu mutane biyu bisa babura tare da tarin harsasai da suka hada da sandunan abubuwa masu fashewa guda 1980. Mutum daga cikinsu ya samu ya tserewa yayin da gudan ya shiga hannu, wani dan asilin Tanda dake jihar Gaya. Mutanen na shirin shigowa birnin Yamai da wadannan boma-bomai. Game da wannan kame ne, ya sa gwamnan yankin Dosso ya bayyana kama kilogram 100 na hodar ibilis na darajar sefa miliyan 28 a makwanni biyu da suka gabata. Baya ga wadannan miyagun kwayoyi, a cewar gwamnan Dosso, birgadiye janar Iro Oumarou, ’yan fashi da makami suna sanya harsasai cikin bududuwa domin a ce man fetur ne ciki. Sanya hannu kan wadannan boma-bamai masu fashewa da ake shirin shiga da su birnin Yamai, wata babbar shaida ce, ta muguwar anniyar abokan gaban kasar Nijar, kuma Allah kadai ya san adadin abubuwa masu fashewa da aka wuce da su, in ji gwamnan yankin Dosso. Amma kuma a cewarsa, bincike zai ci gaba domin gano wadannan mutane da kuma muguwar anniyarsu.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar