logo

HAUSA

Shugaban tarayyar Najeriya ya amince da rahoton Oronsaye wajen hade wasu ma’aikatu wuri guda tare da rushe wasu

2024-02-27 10:42:52 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da aiwatar da rahoton Oronsaye wanda ya bayar da shawarar hade wasu hukumomin gwamnati wuri guda tare kuma da rushe wasu.

Shugaban ya amince da wannan shawara ce yayin taron majalissar zartarwar kasar da ya jagoranta a ranar Litinin 26 ga wata a fadarsa dake birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ne ya kafa kwamitin a shekara ta shekara ta 2012 da nufin yin gyara ga tsarin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, kuma kwamitin ya kasance karkashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikata na tarayyar Mr. Stephen Oronsaye.

Bayan kammala aikinsu, kwamitin ya amince tare da bayar da shawarar rushewa tare da hade wasu hukumomin gwamnati har guda 220 daga cikin 541 da ake da su.

Rahoton kwamitin wanda ya kai yawan shafi 800 ya nuna cewa irin wadannan hukumomin gwamnati ayyukansu suna kama da juna wanda kamata ya yi da jimawa a hade su wuri guda, yayin da wasunsu kuma a sauyawa masu matsayi daga hukuma zuwa sashe, sannan kuma wasu ma a rushe su gaba daya.

Da yake karin haske kan wannan shawara da aka zartar, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na tarayyar Najeriya Muhammed Ibrahim Idris ya bukaci ma’aikatan hukumomin da abin ya shafa da kada su zaci cewa za a kore su ne daga aiki.

“Wannan shiri ba wai yana nufin sallamar mutane daga aikinsu ba ne, amma babban abin da ake bukata shi ne a samar da gwadabe na nuna kwazo a tsakanin ma’aikata sannan kuma gwamnati ta samu damar rage adadin kudaden da take kashewa a wasu bangarorin da suka zama wajibi.”

A yanzu za a hade hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar da hukumar lura da ’yan gudun hijira da mutanen da suka kauracewa muhallansu, sai gidan rediyon tarayya wanda aka hade shi da gidan rediyon muryar Najeriya, yayin da kuma aka mayar da hukumar lura da kyautata rayuwar al’umomin da suke zaune a kan iyakoki zuwa sashe a hukumar lura da iyakoki ta kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)