logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya yi kira da yin takara mai adalci yayin da ake gina kasuwar bai daya ta kasa

2024-02-27 10:57:55 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a samar da sabbin nasarori wajen gina kasuwar kasa ta bai daya domin tallafawa sabon tsarin raya kasa da ma samun ci gaba mai inganci.

Firaministan ya bayyana haka ne yayin wani zaman nazari na majalisar gudanarwar kasar, wanda ya jagoranta a jiya Litinin.

A cewarsa, idan ana son ingiza samar da kasuwar bai daya ta kasa, to ya zama wajibi a yi amfani da fifikon da kasar ke da shi kamar na babbar kasuwa da yalwar albarkatun gina tattalin arziki da cikakken tsarin ayyukan masana’antu da kuma kawar da abubuwan dake kawo tsaiko ga ci gaban tattalin arziki.

Ya kara da cewa, wajibi ne a kawar da manufofi da ka’idojin dake tsaiko ga gina kasuwar bai daya da takara mai adalci. (Fa’iza Mustapha)