logo

HAUSA

Majalisar wakilan jama’a ta kasar Sin ta kammala taron kwamitinta na dindindin

2024-02-27 15:53:39 CMG Hausa

A yau Talata, kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 14, ya kammala taronsa na 8, a birnin Beijing.

Yayin rufe taron, ‘yan majalisar NPC sun kada kuri’ar amincewa da dokar kare sirrikan kasa da aka yi wa garambawul. Kuma shugaba Xi Jinping ya sa hannu kan umarnin zartar da dokar.

Shugaban kwamitin na dindindin na majalisar Zhao Leji ne ya jagoranci zaman rufe taron. (Fa’iza Mustapha)