logo

HAUSA

Rahoto: Kamfanonin waje na da kwarin gwiwa game da kasuwar Sin a 2024

2024-02-27 19:52:00 CMG Hausa

Wani rahoto da kungiyar ‘yan kasuwan Amurka ta kudancin Sin ko “AmCham South China” ta fitar a Talatar nan, ya nuna yadda mafi rinjayen kamfanoni 183 da aka yi nazarin su, suka nuna kwarin gwiwar su ga bunkasar kasuwar Sin a bana.

Rahoton kungiyar ya nuna cewa, cikin kamfanonin, kaso 76 bisa dari na da shirin sake zuba jari a Sin a shekarar nan ta 2024. Cikin wadanda suke da burin zuba jari a Sin a bana, kaso 45 bisa dari sun bayyana fatan mayar da hankali ga sayar da hajoji, da talla, da fannin bunkasa kasuwanci. Sauran sassan sun kunshi bincike da samar da ci gaba, da sarrafa hajoji ta amfani da na’urori masu kwakwalwa, da bunkasa sarrafa kayayyaki.

Rahoton na musamman da ake wallafawa duk shekara game da yanayin kasuwanci a kudancin Sin, ana kallon sa a matsayin muhimmin mizani na nazarin yanayin kasuwanci a kasar Sin.  (Saminu Alhassan)