logo

HAUSA

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta CGTN kan tattalin arzikin kasar Sin: "Kasar Sin" ta gaba har yanzu ita ce Sin!

2024-02-26 16:43:28 CMG Hausa

 "Kasar Sin" ta gaba har yanzu ita ce kasar Sin!  Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nakalto wannan tsokaci na 'yan kasuwar kasar Sin, domin bayyana damar da kasar Sin ke da ita a kasuwannin duniya, a yayin taron koli na shugabannin hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya da tekun Fasifik na shekarar 2023. Bisa binciken da CGTN da jami'ar Renmin ta kasar Sin (RUC) suka gudanar ta cibiyar binciken sadarwar kasa da kasa ta New Era, sama da kashi 90 cikin 100 (90.6%) na masu amsa tambayoyin a duniya sun yaba da cewa, kasar Sin kasa ce mai muhimmanci, kuma zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da kasar Sin na nufin moriyar kansu. Wannan ya zama yarjejeniya ta gama gari a tsakanin kasashen duniya.

Kasar Sin ba za ta iya ci gaba a ware a duniya ba, kuma duniya na bukatar kasar Sin don samun wadata. A ganin masu amsa tambayoyin, kasar Sin ba wai kawai jigo ce ta bunkasa tattalin arzikin duniya da ma ci gaban duniya ba, har ma ta kasance mai tabbatar da daidaito kuma amintacciyar abokiyar huldar kasa da kasa.

Kwarin gwiwar duniya ga tsammanin karfin tattalin arzikin kasar Sin, bai kasance a dalilin girma da kuma daidaiton kasuwar kasar Sin kawai ba, har ma da manufar samar da daidaito da kuma hadin kan samar da ci gaba da kasar Sin ta bi wajen yin mu’amalar musaya da kasashen waje.

A zamaninmu na yau, tun daga tunanin al'ummar duniya na makomar bai daya, daga shirin shawarar “ziri daya da hanya daya”, zuwa shirin bunkasa duniya, da shirin tsaro na duniya, da shirin wayewar duniya, sa’annan zuwa shirin shiga tsakani na Saudiyya da Iran don cimma sulhu mai cike da tarihi, da inganta hadin gwiwar kasa da kasa, da taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya don cimma matsaya ta UAE……Ra'ayoyi, tsare-tsare da hikimar kasar Sin suna kara samun amincewa da fata daga kasashen duniya.(Muhammed Yahaya)