logo

HAUSA

Sin: Hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Rasha ba su da nufin illata wani bangare na daban

2024-02-26 19:25:46 CMG Hausa

A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce har kullum Sin na nacewa matsayi madaidaici na adalci game da rikicin Ukraine, kuma ta sha alwashin yayata burin samar da zaman lafiya.

Mao, wadda ta jagoranci taron ‘yan jarida na rana rana da aka saba gudanarwa, ta yi tsokacin ne bayan matakin da ofishin baitul malin Amurka ya dauka a makon da ya gabata, na sanya wasu kamfanonin Sin 9 cikin jerin kamfanonin da ofishin ya kakabawa takunkumi, bisa zargin su da wai suna taimakawa kasar Rasha, wajen kaucewa takunkuman Amurka da na abokan kawancen ta.

Mao Ning ta kara da cewa, Sin da Rasha na gudanar da cudanyar tattalin arziki da cinikayya, ba tare da hakon wani bangare na daban ban. Kaza lika Sin na matukar adawa da haramtattun takunkumai daga bangare guda kan kamfanonin ta, kuma za ta dauki matakan da suka wajaba, don kare halastattun hakkokinta, da moriyar kamfanonin ta yadda ya kamata. Ta kuma tabbatar da cewa, ci gaban kasar Sin dama ce ga dukkanin duniya, ba wai barazana ga kowa ba.

Game da ziyarar da shugaban kasar Saliyo zai kawo kasar Sin kuwa, Mao Ning ta ce an yi imanin wannan ziyara za ta ingiza sabon kuzari, ga cikakken ci gaba mai zurfi na alakar Sin da Saliyo.  (Saminu Alhassan)