logo

HAUSA

Nijar za ta samu bunkasuwar tattalin arziki mafi karfi a Afrika a shekarar 2024, a cewar bankin BAD

2024-02-26 09:27:30 CMG Hausa

Cibiyar nazarin tattalin arziki da kudi ta Agence Ecofin ta fitar da wasu alkaluma a makon da ya gabata na hasashen bakin ci gaban Afrika BAD dake nuna cewa tattalin arzikin kasar Nijar zai samu bunkasuwa a shekarar 2024.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu ya duba wannan rahoto, ga kuma rahoton da ya hada mana. 

Shi dai wannan rahoto ya fara da cewa a shekarar 2023, Nijar ta kaddamar da aikin bututun mai daga Nijar zuwa Bénin. Wanda shirin zai baiwa Nijar samun wata bunkasuwar tattalin arziki mai armashi bisa ga gajiyar da kasar za ta samu.

A shekarar 2024, Nijar za ta nuna bunkasuwar tattalin arziki mafi karfi a nahiyar Afrika, a cewar alkaluman bankin ci gaban Afrika BAD bisa wani rahoto mai taken kwarewa da hasashen kyautatuwar tattalin arziki a Afrika.

A cewar wannan hasashe, kasar Nijar za ta samu wata bunkasuwa ta kashi 11.2 cikin 100. Inda za ta wuce kasar Sénégal mai kashi 8.2 cikin 100, Libiya mai kashi 7.9 cikin 100, Rwanda mai kashi 7.2 cikin 100 da kuma Cote d'ivoire mai kashi 6.8 cikin 100.

Hakan na da nasaba da shirin kasar na fitar da danyen mai ta bututun Nijar-Benin bisa amfani da tashar ruwan Sème domin saida danyen manta.

Kasar Nijar za ta samu damar fitar dayen manta da zai kai ganga dubu 110 kowace rana sabanin ganga dubu 20 kowace rana a yanzu.

Hasashen BAD ya rubanya har sau uku na tsinkayen bunkasuwa na hukumar kan kasar a shekarar 2023 dake kashi 4.3 cikin 100. Wadannan hasashe na zuwa daidai da hasashen hukumomin kasar Nijar dake kashi 11.3 cikin 100, kamar yadda dokar kasafin kudi ta shekarar 2024 ta kiyasta, dake dogaro bisa dage takunkumi sannu a hankali na kungiyar CEDEAO da UEMOA, haka kuma hasashen na la’akari da kyautatuwar kasuwancin duniya da karfin farashin kayayyakin bukatun yau da kullum da kuma kyautatuwar yanayin tsaro. 

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.