logo

HAUSA

Kasuwar wayar salula da ake iya nadewa ta samu bunkasa a 2023 a kasar Sin

2024-02-26 13:32:37 CMG Hausa

Yawan wayoyin salula na zamani da ake iya nadewa, wadanda aka yi oda tare da jigilarsu daga kasuwar kasar Sin, ya habaka a shekarar 2023 da kaso 114.5

Wani rahoto da wata cibiyar nazari da tattara bayanan kasuwar duniya ta fitar, ta ce yawan wayoyin da aka yi oda da jigila ya zarce miliyan 7 a bara, lamarin da ya sa aka samu karuwar kaso 100 bisa 100 a kowacce shekara cikin shekaru 4 jere.

Rahoton ya alakanta ci gaban da aka samu da karuwar gogewar masu sayayya wajen amfani da wayoyin da kuma raguwar farashinsu.

A shekarar 2023, irin wayoyin salula na zamani da ake iya nadewa, wadanda farashinsu ya kai dala 1,000 ko fiye, su ne suka mamaye kaso 66.5 na sayayya a kasuwar, adadin da ya ragu daga kaso 81 da ya kasance a shekarar 2022. (Fa’iza Mustapha)