logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta dauki kwararan matakai na ingiza cimma nasarar tsagaita wuta a Gaza

2024-02-26 21:18:10 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi kira ga Amurka da ta saurari kiraye-kirayen sassan kasa da kasa, na tabbatar da an kai ga tsagaita wuta a zirin Gaza, ta kuma taka rawar gani wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, da saukaka matsalolin jin kai da ake fuskanta.

Mao Ning ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na Litinin 26 ga watan nan, lokacin da take amsa tambayar da aka yi mata game da wani rahoto, wanda ke cewa a yayin taron ministocin kungiyar G20 da ya gabata a baya bayan nan, kasashe da dama sun soki Amurka bisa yadda ta nuna adawa da kudurin tsagaita bude wuta a zirin Gaza. (Saminu Alhassan)