logo

HAUSA

Shugaban kasar Saliyo zai kawo ziyara a kasar Sin

2024-02-26 15:03:12 CMG Hausa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio zai kawo ziyara a kasar Sin tun daga ranar 27 ga watan Febrairu zuwa ranar 2 ga watan Maris.

An haifi Julius Maada Bio a watan Mayu na shekarar 1964, ya shiga jam’iyyar jama’ar kasar Saliyo a shekarar 2005, kuma a watan Afrilu na shekarar 2018, ya zama shugaban kasar Saliyo, kana ya samu zarcewa a karo na biyu a matsayin shugaban kasar a watan Yuni na shekarar 2023.

Shugaba Bio ya taba zuwa kasar Sin inda ya shafe kusan wata guda tun daga watan Agusta zuwa Satumba na shekarar 2018 don halartar taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka na FOCAC tare da kuma yin ziyarar aiki a kasar Sin. A watan Mayu na shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya buga masa waya don taya shi murnar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)