logo

HAUSA

Sin ta ki amincewa da Amurka ta saka takunkumi ga kamfanonin Sin da dama dake da alaka da kasar Rasha

2024-02-26 15:20:13 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ya yi hira da ‘yan jarida a yau kan takunkumin da Amurka ta kakabawa kamfanonin Sin da dama masu alaka da kasar Rasha, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana sane da wannan batu. Matakin da kasar Amurka ta dauka na kakaba takunkumi bisa son ranta, da tsoma baki cikin harkokin kasashe da yin matsin lamba a fannin tattalin arziki, ya sabawa ka’idoji da tsarin tattalin arziki da cinikayya na duniya, da kawo illa ga samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata. Don haka Sin ta ki amincewa da wannan batu. (Zainab Zhang)