logo

HAUSA

An gudanar da taro na 8 na zaunannen kwamitin wakilin jama’ar kasar Sin karo na 14 a Beijing

2024-02-26 14:00:10 CMG Hausa

Yau da safe a babban dakin taron jama’a dake nan birnin Beijing, an gudanar da zaman farko na taro na 8 na zaunannen kwamitin wakilin jama’ar kasar Sin karo na 14.

Maudu’in gudanar da zaman farko na zaunannen kwamitin shi ne shirya zama na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, inda aka yi bincike kan rahoton aikin zaunannen kwamitin, da daftarin ajandar zama na biyu na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 da daftarin jerin sunayen tawagogin shugabanni da manyan sakatarori da mahalartar zaman da sauransu, wadanda aka gabatar a taron shugabannin kwamitin. (Zainab Zhang)