logo

HAUSA

Kungiyar Ecowas ta cire takunkumin da ta kakabawa kasashen Niger, Burkina Faso, Mali da kuma Guinea

2024-02-25 15:14:19 CGTN HAUSA

 

Kungiyar Ecowas ta bukaci kasashen Mali da Niger da Burkina Faso da kuma Guinea da su duba yiwuwar sauya tunaninsu na ficewa daga cikin kungiyar.

Bukatar hakan na kunshe ne cikin takardar bayanin bayan taron gaggawa da kungiyar ta gudanar a birnin Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Najeriya, bayan da ta sanar da cire takunkumin da ta sanyawa kasashen hudu.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.