logo

HAUSA

Shagalin murnar bikin fitilu da CMG ya gabatar ya samu matukar karbuwa daga jama’ar Sin da waje

2024-02-25 20:55:06 CGTN HAUSA

 

A jiya Asabar 24 ga wata, kafar CMG ta gabatar da kasaitaccen shagalin murnar bikin nune-nunen fitilu ta kasar Sin ko “Lantern Festival” na shekarar 2024 cikin nasara. Wannan biki mai kunshe da shirye-shiryen yada al’adu, da fasahohi, da kirkire-kirkire tare, ya samun karbuwa matuka daga jama’ar Sin da waje.

Bisa alkaluman da aka bayar, ya zuwa karfe 8 na safiyar yau, yawan mutanen da suka kalli wannan bikin da aka gabatar kai tsaye ta nau’o’in allunan nuna fina-finai daban-daban ya kai miliyan 353, kana ta yanar gizo kuma, adadin ya kai miliyan 184, a bangaren talibiji kuma adadin ya kai miliyan 169, kuma dukkan wadannan alkaluma sun zarce na bara.

Kaza lika yawan mutanen da suka karanta labaran dake da nasaba da wannan biki a shafukan sada zumunta na yanar gizo ya kai biliyan 2.99, kuma yawan mutanen da suka kalli bidiyoyin dake da nasaba da wannan biki a kan yanar gizo ko wayar salula ya kai miliyan 250. (Amina Xu)