logo

HAUSA

Bankin raya noma na Sin ya fitar da tsare-tsaren bunkasa karkara

2024-02-25 15:47:54 CMG Hausa

Bankin raya noma na kasar Sin, ya fitar da tsarin bunkasa samar da rance, da nufin farfado yankunan karkara ba tare da gurbata muhalli ba. Bankin ya ce zai mayar da hankali ga biyan bukatun mazauna karkara, ta fannin samar da kudade ga muhimman sassa, ciki har da bangaren kyautata rayuwar al’umma, da zamanantar da harkar noma da yankunan karkara, yayin da a daya hannun zai lalubo managartan hanyoyin tallafawa da kudade don cin cikakkiyar gajiyar shirin.

Bankin ya ce zai dora muhimmanci ga sashen tallafawa rayuwar mazauna karkara, da ba da kariya ga muhallin halittu, da fadada samar da ababen more rayuwa, da na ba da hidima a yankunan karkara, da ma gina kauyuka masu cin gajiyar kafafen yanar gizo.

Bankin ya kara da cewa, a shekarar 2023 da ta gabata, ya samar da rance da yawan sa ya kai yuan biliyan 488, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 68.67 ga shirye shiryen farfado da kauyuka ba tare da gurbata muhalli ba.   (Saminu Alhassan)