logo

HAUSA

CMG zai watsa shagalin bikin fitilu na shekarar 2024 a daren yau

2024-02-24 16:38:46 CMG Hausa

 

Da misalin karfe 8 na yammacin yau ne, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG zai watsa shagalin bikin fitilu da ake kira "Lantern Festival Gala 2024" don masu kallo dake cikin gida da wajen kasar Sin. Za a gudanar da shagalin ne ta hanyar nuna wake-wake, da raye-raye, da wasan kwaikwayo, da sauran nau'o'in shirye-shirye, ta yadda Sinawan dake fadin duniya za su ji dadin kallon nau’o’in fitilun, da hasashen kacici-kacici na fitilu, da kuma jin dadin bikin baki daya.((brahim)