logo

HAUSA

Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Gwajin Fasahar Sadarwa

2024-02-24 15:35:39 CMG Hausa

A jiya ne, kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na gwajin fasahar sadarwa zuwa sararin samaniya, daga cibiyar harba taurarin dan Adam na Wenchang a lardin Hainan dake kudancin tsibirin Hainan.

An harba tauraron ne da karfe 7 da mituna 30 na yamma, agogon birnin Beijing, ta hanyar amfani da rokar Long March-5 Y7 kuma ya shiga cikin falaki kamar yadda aka tsara.

Za a yi amfani da tauraron ne wajen gwaje-gwajen fasahar sadarwa mai saurin gaske.

Wannan shi ne karo na 509 da aka yi amfani da rokar Long March, wajen harba taurarin dan Adam.(Ibrahim)