logo

HAUSA

Jamhuriyar Congo tana son karfafa zumunta da hadin gwiwa da Sin

2024-02-24 16:26:46 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar jamhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso ya bayyana a jiya cewa, kasarsa tana son yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen karfafa dadadden zumunci da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

An gudanar da liyafar murnar cika shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da jamhuriyar Congo a wannan rana a fadar shugaban jamhuriyar Congo dake birnin Brazzaville, inda minista Gakosso ya bayyana cewa, dangantakar Congo da Sin ta samu ci gaba sosai cikin shekaru 60 da suka gabata. Bangaren jamhuriyar Congo yana martaba ka'idar Sin daya tak a duniya, jamhuriyar Congo da Sin sun amince da juna da kuma yin hadin gwiwa a dukkan fannoni don amfanawa jama’ar kasashen biyu baki daya.

A nasa bangare, jakadan Sin dake jamhuriyar Congo Li Yan ya yi jawabin cewa, a cikin shekaru 60 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da jamhuriyar Congo, kasashen biyu sun nuna goyon baya da hadin gwiwa da juna, sun kasance abin misali na hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka. A matsayin wani sabon mafari na tarihi, kamata ya yi dukkan bangarorin biyu su aiwatar da muhimman shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma bisa la'akari da ci gaba da kasancewa masu tabbatar da gaskiya da adalci, masu amana iri daya, abokan hadin gwiwar samun nasara, da yin mu'amala da koyi da juna, da karfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kafa ginshikin cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da ba da babbar gudummawa ga manyan al'ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma, da kuma al'umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga daukacin bil-Adama (Zainab Zhang)