logo

HAUSA

Aleksandar Vučić: yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci a tsakanin Sin da Serbia ta bude sabuwar kofa ga bunkasuwar Serbia

2024-02-24 20:40:00 CMG Hausa

Shugaban kasar Serbia Aleksandar Vučić ya yi hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin kasar Sin wato CMG a kwanakin baya, inda ya bayyana fatan cewa, yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci da aka daddale tsakanin Sin da Serbia za ta bude sabuwar kofar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Vučić ya yi nuni da cewa, yarjejeniyar da kasashen Sin da Serbia suka daddale a watan Oktoban bara, za ta kawo sabbin damammaki marasa adadi ga Serbia. Ya yi imani da cewa, yarjejeniyar za ta kawo moriya ga kasar Sin, amma ta fi kawo moriya ga kasar Serbia. Za kuma ta bude wata babbar kasuwa ga kasar Serbia a fannin amfanin gona. A sa'i daya kuma, Serbia na iya shigo da kayayyakin kasar Sin a farashi mai rahusa, kana karin kamfanoni da jama'ar kasar Sin za su je kasar Serbia domin yin hadin gwiwa tsakanin kamfanoni da ma'aikata, ta yadda za su bude wata sabuwar kofa ga ci gaban kasar Serbia. (Zainab Zhang)