logo

HAUSA

Babban Jami'in JKS Ya Bukaci A Himmantu Wajen Ciyar Da Kokarin Dunkulewar Kasar Gaba

2024-02-23 20:02:04 CMG Hausa

Babban jami'in Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin CPC, Wang Huning ya bukaci da a zage damtse wajen ciyar da manufar sake hadewar kasa gaba.

Wang, mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS, kuma shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya bayyana haka ne a yayin wani taro kan harkokin yankin Taiwan da aka gudanar a ranakun Alhamis zuwa yau Jumma'a a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Wang ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin jam'iyyar na warware batun Taiwan a sabon zamani da shawarwari da tsare-tsaren da kwamitin kolin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yanke kan ayyukan da suka shafi Taiwan.(Ibrahim)