logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Bukatar Kara Sabunta Kayan Aiki Da Kayayyakin Masarufi

2024-02-23 20:54:59 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada bukatar inganta wani sabon zagaye na sabunta manyan na'urori da kayayyakin masarufi, da rage farashin jigilar kayayyaki.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana haka ne a yayin da ya jagoranci taron kwamitin kolin kula da harkokin kudi da tattalin arziki.(Ibrahim)