logo

HAUSA

An kaddamar da watan ingiza sayayya na shekarar 2024 a Beijing

2024-02-23 10:51:59 CGTN HAUSA

 

An yi bikin kaddamar da watan ingzia sayayya, kana bikin sayayya na yankunan Beijing da Tianjin da lardin Heibei na shekarar 2024 a nan birnin Beijing.

Ma’aikatar kasuwancin Sin ta mai da shekarar 2024 a matsayin shekarar ingiza sayayya, inda ta gabatar da jerin manufofin habaka bukatun gida da ingiza sayayya, tare da gabatar da mabambanta ayyukan sayar da kayayyaki. Wannan ne watan ingiza sayayya, irinsa na farko da aka gabatar bayan Bikin Bazara a duk fadin kasar, za a yi la’akari da kayayyaki kirar kasar Sin dake shahara matuka tsakanin matasa, da kuma ba da jagoranci ga wurare daban-daban da su hada kayayyakinsu tare da al’adu da yanayin da ake ciki, ta yadda za a biya bukatun jama’a bisa halin da ake ciki. Ban da wannan kuma, za a samar da ingatattun kayayyaki da hidimomi, da kuma ingiza hada kasuwa a zahiri da ta yanar gizo tare don biyan bukatun jama’a. (Amina Xu)