logo

HAUSA

Yakubu Gawon ya bukaci kungiyar Ecowas da ta cire takunkumi ga wasu kasashe

2024-02-23 09:15:40 CMG Hausa

Tsohon shugaban sojin Najeriya Janaral Yakubu Gawon ga gabatar da bukata ga kungiyar Ecowas na neman cire takunkumin da ta kakabawa kasashen Mali, Burkina faso da Jamhuriyyar Nijar.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a hedikwatar hukumar gudanarwar kungiyar dake birnin Abuja, ya ce, cire takunkumin shi ne matakin farko da zai kai ga warware rigigimun siyasa da suka dabaibaye kasashen uku.

Daga tarayayr Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Tsohon shugaban kasar na tarayyar Najeriya ya ce, manufar samar da ita wannan kungiya ta Ecowas a 1975 shi ne ta habaka tattalin arziki da hadin kan mambobin kasashe, amma ba kirkirar matsalolin da za su kai ga durkasar da tattalin arzikin kasashen ba.

Janaral Yakubu Gawon mai ritaya ya bayyana damuwa bisa kudurin kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar na neman ficewa daga kungiyar, lamarin da ya bayyana da cewa, babban barazana ne ga hadin kan kungiyar, sannan kuma illa ne ga rayuwar talakawan dake zaune a kasashen.

“Ya zama wajibi a gare ni na yi magana a madadin shugabannin kasashe 14 da muka kasance tare da su a birnin Legos a ranar 27 ga watan Mayun 1975 domin kafa kungiyar Ecowas, wannan kungiyar hakika ta sami cimma nasarori da dama tun bayan kafuwarta, wadanda suka hada da fadada harkokin cinikayya, baiwa ’yan kasashen yammacin Afrika damar zama cikin kowacce kasa dake cikin kungiyar, da kuma samun nasara a shirin wanzar da zaman lafiya a kasashen Liberiya da kuma Saliyo, duk da ’yan matsalolin da ake fuskanta. Kungiyar ta Ecowas ta zama abar misali wajen tabbatar da hadin kai ga sauran nahiyoyi.”

Janaral Yakubu Gawon ya kara kira ga shugabannin kasashen yammacin Afrika tare da na kasashe ukun da ake da matsala a kan su da su hada kai domin samar da dauwamammen zama lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar. (Garba Abdullahi Bagwai)