logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da manazarcin harkokin waje na shugaban gwamnatin Jamus

2024-02-23 20:26:31 CMG Hausa

A yau ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da mai baiwa shugaban gwamnatin kasar Jamus shawara kan harkokin waje Jens Plötner a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A yayin ganawar, Wang Yi ya ce, bunkasuwar kasashen Sin da Jamus wata dama ce, maimakon kalubale ga juna. Ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da fahimtar juna, da ci gaba da inganta hadin gwiwa ba tare da rufa-rufa ba da martaba ka'idojin kasuwa, da taimakawa ci gaban tattalin arzikin kasashen biyu, har ma farfado da tattalin arzikin duniya baki daya. Bai kamata a bi ra’ayin kawar da hadari da kin yin hadin gwiwa tare da Sin ba. Ya kamata kasashen Sin da Jamus su sa kaimi ga al'ummomin kasa da kasa, don karfafa hadin kai da kyautata tsarin tafiyar da harkokin kasa da kasa, da ba da gudummawa mai kyau wajen tabbatar da zaman lafiya, da ci gaba da wadata a duniya.

A nasa bangare, Plötner ya bayyana cewa, Jamus na mai da hankali sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da yin nazari mai kyau kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Jamus da Sin, tana mai tabbatarwa da nuna godiya ga nasarorin da kasar Sin ta samu, kana tana farin cikin ganin kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a tsakanin kasashen duniya. Jamus na fatan karfafa yin shawarwari tare da kasar Sin bisa manyan tsare-tsare, da kara fadada hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da ba da sabbin gudummawa wajen tinkarar matsalar sauyin yanayi, da sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya, da cimma moriyar juna da samun moriyar juna. (Zainab Zhang)