logo

HAUSA

AU ta bayyana damuwa game da rikici a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

2024-02-23 11:11:21 CMG Hausa

Shugaban hukumar kula da ayyukan Tarayyar Afrika (AU) Musa Faki Mahamat, ya yi kira da a tsagaita rikicin dake ci gaba da karuwa a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo (DRC).

Cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin Laraba, Musa Faki Mahamat ya ce wajibi ne a kare cikakken mutunci da tsaro da ‘yanci da kwanciyar hankali da rayukan fararen hula na dukkan kasashen yankin.

Ya kara da cewa, babu wani matakin soji da zai kawo karshen matsaloli da takaddama tsakanin al’ummar nahiyar Afrika. Yana mai kira ga manyan kasashe da su kauracewa tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen Afrika, musammam na yankin manyan tabkuna.

A ranar Asabar ne, rundunar sojin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta zargi Rwanda da kaddamar da hari da jirgi maras matuki kan filin jirgin saman Goma, babban birnin lardin North Kivu, inda ake gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da ‘yan tawayen kungiyar M23. (Fa’iza Mustapha)