logo

HAUSA

Sin Ta Samu Karuwar Kudaden Da Aka Kashe A Fannin Yin Sayayya A Lokacin Hutun Bikin Bazara

2024-02-22 20:55:37 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin He Yadong ya bayyana yau Alhamis din nan cewa, an samu karuwar sayayya a lokacin hutun bikin Bazara, alamu na fara samun bunkasuwa mai kyau a shekarar 2024.

Jami’in ya ce, akwai alamomi masu kyau a fannin kayayyakin masarufi a lokacin hutun. Ya ba da misali da alkaluman kamfanonin sayar da hajoji da ma’aikatar ta sanya wa ido, inda yawan zinare da azurfa da kayan adon da aka sayar ya karu da kashi 23.8 cikin 100, kayayyakin wasannin motsa jiki da nishadi sun karu da kashi 15.6 cikin 100, yayin da kayayyakin sadarwa suka karu da kashi 10.4 cikin 100.

He ya ce, bangaren hidima na kasar Sin ya samu ci gaba mai karfi a wannan lokaci. Yana mai cewa, masu yawon bude ido na cikin gida sun kashe kudaden da suka kai yuan biliyan 632.69, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 89, wadanda suka karu da kashi 47.3 cikin 100 a kan na shekarar bara, yayin da gidajen sinima suka samu kudaden da yawansu ya kai yuan biliyan 8.02 a lokacin hutun. (Ibrahim)