logo

HAUSA

Wadanda suka mutu sakamakon zazzabin Lassa sun kai 14 a kudancin Najeriya

2024-02-22 09:26:13 CMG Hausa

Adadin wadanda suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya ya karu daga 10 zuwa 14 tun daga farkon shekarar nan, a cewar hukumar kula da lafiyar jama’a a jiya Laraba.

Mutane 14 da suka mutu na daga cikin mutane 29 da aka tabbatar sun kamu da cutar zazzabin ta Lassa tun daga bullarta ya zuwa ranar Talata, kamar yadda daraktan kula da lafiyar jama’a a Ebonyi Hyacinth Ebenyi, ya shaida wa manema labarai a Abakalilki, babban birnin jihar.

Akalla mutane 110 ne ake zargin sun kamu da cutar a Ebonyi tun daga farkon shekarar nan, kuma “An samu karuwar masu dauke da cutar zazzabin Lassa, kuma tana yaduwa a jihar,” a cewar Ebenyi. (Yahaya)