logo

HAUSA

Nijar kan tsakiyar tattaunawa tsakanin tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

2024-02-22 10:44:40 CMG Hausa

A ranar jiya Laraba 21 ga watan Fabrairun shekarar 2024, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, inda batun kasar Nijar ya kakace ganawar manyan shugabannin biyu.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba wannan batu ga kuma rahoton da ya hada mana. 

Shi dai Yakubu Gowon, tsohon shugaban tarayyar Najeriya ya yi mulkin wannan babbar kasa mafi yawan jama’a a yammacin Afrika daga shekarar 1966 zuwa shekarar 1975. Bisa wannan matsayi ne, tsohon shugaban tarayyar Najeriya ya nemi wannan ganawa tare da shugaban tarayyar Najeriya mai ci Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa dake birnin Abuja.

A tsawon wannan ganawa tasu, shugabannin biyu sun mai da hankali kan batun dage takunkumin da aka sanya wa makwabciyar kasar Nijar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, wanda daga bisa kungiyar ci gaban tattalin azikin kasashen yammacin Afrika CEDEAO ko ECOWAS da kuma kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika UEMOA suka kakkabawa Nijar takunkumi tun yau da kusan watanni 7.

Manyan jami’an biyu sun mai da hankali wajen ingiza tattaunawa tare da kasar Nijar ganin cewa ita ce hanya mafi dacewa domin karfafa zumunci da tarihi dake akwai tun fil’azal tsakanin kasashen biyu dake raba al’umma guda, al’adu guda da kuma shiyya guda.

A idon yawancin ’yan Najeriya da ’yan Nijar, wannan manufa ta tsohon shugaban Najeriya Yakubu Gowon na da fa’ida da alfanu wajen kawo karshen wannan rikici ta yadda dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da dorewa cikin girmama juna.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriiyar Nijar.