logo

HAUSA

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Sayar Wa Taiwan Makamai

2024-02-22 19:20:47 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bukaci Amurka da ta daina sayar da makamai da yin huldar soja da yankin Taiwan.

A cewar rahotanni, ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da sayarwa yankin Taiwan tsarin tattara bayanai na zamani da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 75.

Da take karin haske kan batun, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta shaida wa manema labarai cewa, irin wannan makami da Amurka ke sayarwa yankin na Taiwan, ya keta ikon mallakin kai da ma tsaron kasar Sin, kuma suna illa matuka ga hadin gwiwar Sin da Amurka da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, kuma Sin na adawa da hakan.

Mao ta ce, Sin ta bukaci Amurka da ta mutunta ka'idar “Sin daya tilo a duniya” da sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da kasashen biyu suka cimma a tsakaninsu, ta kuma dakatar da sayar da makamai da yin huldar soji da Taiwan, da kuma dakatar da aikata abubuwan da za su iya tada hankula a mashigin tekun Taiwan.

Ta kara da cewa, kasar Sin za ta dauki kwararan matakan da suka dace don kiyaye ‘yancin kai da cikakkun yankunanta.(Ibrahim)