logo

HAUSA

Nahiyar Turai muhimmin yanki ne da Sin ta mai da hankali musamman a harkokin diplomasiyya

2024-02-22 19:59:34 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau cewa, nahiyar Turai muhimmin yanki ne da kasar Sin ta mai da hankali musamman a harkokin diplomasiyya, kana muhimmiyar abokiya ce ta kasar Sin yayin da take kokarin cimma burin zamanintar da kasar. Bayan shekaru 20 na hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da kungiyar EU, bangarorin biyu sun yi kokarin sa kaimi ga yada ra’ayin bangarori daban daban a duniya da ra’ayin raya kasuwar duniya bisa tsarin bai daya da kuma kiyaye al’adu iri iri a duniya. Yayin da duniya ta shiga wani sabon yanayi na tashin hankali da sauye-sauye, muhimmancin dabaru da tasirin huldar dake tsakanin kasashen Sin da EU na kara yin fice a duniya.

Mao Ning ta kara da cewa, bangarorin biyu za su kiyaye dangantakar abokantaka dake tsakaninsu, da raya hadin gwiwarsu tare da amincewa bambance-bambancen dake tsakaninsu, don sa kaimi ga ci gaba da bunkasuwar dangantakar Sin da Tarayyar Turai cikin dogon lokaci. (Zainab Zhang)