logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kafa tsarin ba da agajin gaggawa na yau da kullum don inganta sakamakon kawar da kangin talauci

2024-02-22 12:21:38 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar harkokin aikin noma da raya kauyuka ta kasar Sin, Tang Renjian, ya bayyana jiya Laraba cewa, ya kamata a mai da hankali kan karfafa ci gaban sassan kawar da kangin talauci, da al’ummun da suka fita daga talauci, a kuma ci gaba da karfafa sa ido da taimako, don hana komawa cikin talauci, da kuma kafa tsarin ba da agajin gaggawa na yau da kullum ga rukunonin mutane masu karancin kudin shiga a kauyuka da yankuna marasa ci gaba.

Ya ce dole ne a tsaya tsayin daka wajen tabbatar da nasarar hana mutane masu yawa sake koma cikin kangin talauci.

Ma’aikatar harkokin aikin noma da raya kauyuka ta kasar ta gudanar da taron aiki na ingantawa, da bunkasa sakamakon kawar da kangin talauci a birnin Longnan dake lardin Gansu. Yayin taron, an bayyana cewa, bayan samun babbar nasara a yakin kawar da kangin talauci, kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yanke shawarar kafa wa’adin wucin gadi na shekaru 5, mai kunshe da wanzar da sakamakon kawar da kangin talauci da farfado da kauyuka.

Bana shekara ce ta hudu cikin zangon wucin gadi na shekaru 5, wanda a cikinsa ake fuskantar sabon sauyin ayyukan ingantawa, da bunkasa sakamakon kawar da kangin talauci. Don haka kamata ya yi a tattara albarkatu, don nuna goyon baya ga yankunan dake kawar da kangin talauci don ganin sun samu ci gaba, kana kuma al’ummunsu su kara samun kudin shiga, ta yadda za a aza harsashi mai inganci, na inganta farfadowar kauyuka, da kuma kafa kasar aikin noma mai inganci cikin sauri. (Safiyah Ma)