logo

HAUSA

An yi kira ga kasashen Afirka da su rungumi tsarin tantance al’umma na dijital domin bunkasa tattalin arziki

2024-02-22 09:52:01 CMG Hausa

Kwararru a fannonin kididdiga da tattara bayanai na Afirka, sun yi kira ga gwamnatocin kasashen nahiyar da su rungumi tsarin tantance al’umma na dijital ko “digital ID”, ta yadda hakan zai bayar da damar bunkasa hada hadar tattalin arziki da yawan ta zai kai kaso 3 zuwa 7, na jimillar ma’aunin raya tattalin arzikin su na GDP.

Kwararrun sun yi kiran ne yayin taron karawa juna sani na “StatsTalk-Africa” karo na 12, wanda cibiyar kididdiga karkashin hukumar raya tattalin arzikin Afirka ta MDD UNECA ta shirya.

Taron na wannan karo dai na da taken "Gina tsarin tantance al’umma na dijital na bai daya, hade tsarin tantance al’umma na dijital da tsarin tantance al’umma don kiyaye doka".

Da yake tsokaci yayin taron na ranar Talata, babban jami’in sashen kirkire-kirkire da raya fasahohi na hukumar UNECA Mactar Seck, ya ce tsarin tantance al’umma na dijital, zai iya samar da dama ta bunkasa tattalin arziki ga kasashe, musamman ta hanyar kyautata gudanar hada hadar tattalin arziki, da ingiza tsarin sada dukkanin sassan al’umma da fannonin samar da hidimomi, da bayar da damar mayar da cudanyar harkoki masu kima kan tsarin dijital, musamman wadanda ke da bukatar amincewa juna bisa matsayin koli.  (Saminu Alhassan)