Amurka ta zama babban cikas ga dakile yakin Gaza bayan da ta hau kujerar na ki
2024-02-22 11:01:22 CMG Hausa
Amurka ta sake jefa kuri’ar kin amincewa da daftarin kudurin tsagaita wuta a Gaza, wanda aka gabatar gaban kwamitin sulhun MDD a ranar 20 ga watan nan.
Daftarin kudurin wanda kasar Aljeriya ta gabatar a madadin kasashen Larabawa, ya bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Gaza, da sakin dukkan mutanen da ake tsare da su, da shigar da kayayyakin jin kai, da kuma hana tilastawa jama’a canja matsuguni. Hakan ba wai kawai matsaya guda ce da kwamitin sulhun MDD ya cimma ba, har ma mataki ne guda daya da kasa da kasa suka cimmawa da nufin tabbatar da tsagaita wuta da daina yaki.
Amurka ta yi amfani da ikon jefa kuri’ar kin amincewa sau da yawa. Kaza lika, tun bayan barkewar wani sabon zagaye na rikicin Falasdinu da Isra'ila a watan Oktoba na shekarar 2023, kwamitin sulhun MDD ya kada kuri’a sau 8 game da batun Falasditu da Isra’ila, sai dai kawo yanzu an zartas da kuduri guda biyu ne kacal.
A wannan karo ma, Amurka ta raina rayuwar fararen hula a Gaza, ta yi amfani da ikon jefa kuri’ar kin amincewa, inda ta zama babban cikas ga aikin kwamitin sulhun MDD na gudanar da ayyukansa.
Mummunan tasiri da rikicin Falasdinu da Isra’ila ke yi ya ci gaba da hauhawa. A yayin da Amurka ke ci gaba da hawa kujerar na ki game da daftarin kudirorin tsagaita wuta tsakanin Falasdinu da Isra'ila a kwamitin sulhu na MDD, tana kuma ci gaba da ba da taimakon soji ga Isra'ila, lamarin da ya taimaka wajen yaduwa da kuma tsanantar rikicin, don haka ta zamo bangare mafi daukar alhakin yanayi mai hatsari da ake ciki a Gabas ta Tsakiya. (Safiyah Ma)