logo

HAUSA

BRICS Na Samun Karbuwa Daga Kasashen Da Tattalin Arzikinsu Ke Bunkasa Da Kasashe Masu Tasowa

2024-02-22 19:37:10 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba yi Alhamis din nan cewa, a duniyar yau da ake ci gaba da fuskantar kasada da kalubale, kasashe masu tasowa suna kara neman hadin kai da ci gaba, da nuna adawa da tsoma baki daga waje, da neman karfi ta hanyar hadin kai. Saboda haka, BRICS na samun karbuwa daga kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa gami da kasashe masu tasowa, kuma ta zama mai inganci, kwanciyar hankali da ci gaba a cikin harkokin kasa da kasa.

Mao Ning ta ce, kasar Sin tana son yin aiki tare da dukkan bangarori, don ci gaba da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da kara fadada hadin gwiwa a aikace a fannoni daban daban, da taimakawa wajen tabbatar da daidaito da adalci a tsarin tafiyar da harkokin duniya da kara ba da gudummawar BRICS ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.(Ibrahim)