logo

HAUSA

Cibyar dakon kaya da kasar Sin ta gina na taimakawa bunkasar kayayyakin da ake fitarwa a kasar Uganda

2024-02-21 14:20:03 CMG Hausa

Cibiyar jigilar kayayyaki da kasar Sin ta gina a filin jirgin sama na Entebebe na kasar Uganda, na taimakawa wajen bunkasa kayayyakin da ake fitarwa daga kasar ta gabashin Afirka, a cewar cibiyar kula da harkokin sufurin sama na kasar a jiya Talata.

Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Uganda Vianney Luggya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sabuwar cibiyar ya fi girma idan aka kwatanta da na da.

"Mun fara amfani da sabuwar cibiyar dakon kaya ne a shekarar 2021. Wannan ita ce shekara ta uku da ake amfani da ita. Tabbas, ta fi saukakawa saboda tana iya daukar tan 100,000 na kaya a shekara," a cewar Luggya.

Alkaluman da UCAA ta fitar sun nuna cewa an sarrafa fiye da tan 40,000 na kayayyaki da aka yi jigilarsu zuwa kasashen waje a cibiyar a bara, idan aka kwatanta da tan 39,000 na kayayyakin da ake fitarwa da aka sarrafa a shekarar 2021. (Muhammed Yahaya)