logo

HAUSA

Sin Na Fatan Kara Yin Hadin Gwiwa Da Bankin Duniya

2024-02-21 19:04:42 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin na fatan zurfafa hadin gwiwa da bankin duniya, da ba da gudummawa mai kyau wajen rage talauci a duniya da samun bunkasuwa.

Mao Ning ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na yau da kullum Larabar nan lokacin da aka bukaci ta yi karin haske kan nadin Zhang Wencai da bankin ya yi a matsayin sabon manajan darakta kuma babban jami’in gudanarwa na rukunin bankin duniya.

Mao ta ce, muna maraba da nadin da bankin ya yi, tana mai nuni da cewa, kasar Sin kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, kuma bankin duniya shi ne cibiyar raya kasa da kasa mafi girma a duniya. Bangarorin biyu sun kulla kawancen ci gaba na kud-da-kud, tare da gudanar da hadin gwiwa mai inganci cikin shekaru 40 da suka gabata.

Ta ce, kasar Sin tana goyon bayan yi wa bankin duniya gyare-gyare, don karfafa manufarsa ta samun bunkasuwa, da kara karfinsa, da taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba mai dorewa, da magance kalubalen da duniya ke fuskanta yadda ya kamata.(Ibrahim)