logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jaddada bukatar aiwatar da matakan kyautata tsarin lura da filaye domin cin gajiyarsu yadda ya kamata

2024-02-21 10:14:33 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada bukatar kafawa, da kuma kyautata tsarin lura da albarkatun filaye dake sassan kasar Sin, ta yadda hakan zai bayar da damar hade moriyarsu da manyan manufofin raya tattalin arzikin kasa, da ci gaban yankuna, tare da samun zarafin rarraba moriyar filayen yadda ya kamata da cin babbar gajiya daga gare su.

A ranar Litinin 19 ga watan nan ne shugaba Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 4 na hukumar koli mai aikin zurfafa cikakkun sauye-sauye, a matsayinsa na daraktan hukumar. Yayin zaman an yi nazari tare da amincewa da takardu da dama, wadanda suka shafi ka’idojin gudanar da sauye-sauye a fannin ba da jagoranci game da lura da filaye, domin ingiza damar ba da tabbacin samun ci gaba mai inganci a yankunan dake da fifikon karfin takara, da dokokin bunkasa cikakken tsarin sauya akala zuwa kyautata muhalli, don bunkasa tattakin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma da dai sauransu.

Ya ce tabbatar da sauya akala zuwa ga tsarin kyautata muhalli daga dukkanin fannonin tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al’umma, muhimmin jigo ne na shawo kan kalubalen raba albarkatu, da muhalli da muhallin halittu. Kana yana da muhimmanci wajen ingiza cikakken tsarin aiwatar da sauyi, madaidaici, mai kunshe da kirkire-kirkire da tsaro.  (Saminu Alhassan)