logo

HAUSA

Matakin Amurka Ya Jefa Al'ummar Gaza Cikin Wani Yanayi Mai Hadari

2024-02-21 20:01:00 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a taron manema labaru yau Laraba cewa, Amurka ta sake yin fatali da daftarin kudurin kwamitin sulhu na MDD kan zirin Gaza, lamarin da ya sa al'ummar Gaza cikin wani yanayi mai hadari.

A jiya ne dai, Amurka ta sake kada kuri'ar kin amincewa da daftarin kudurin da kasar Aljeriya ta gabatar na neman tsagaita bude wuta na jin kai cikin gaggawa a zirin Gaza. Da take karin haske kan wannan tambaya, Mao Ning ta yi nuni da cewa, halin da ake ciki na jin kai a Gaza, yana da matukar muni, kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin ya yi tasiri sosai. Tilas ne kwamitin sulhun ya dauki matakai cikin gaggawa don inganta tsagaita bude wuta da kuma kawo karshen yakin.

Mao ta ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da dukkan bangarori na kasa da kasa, wajen ingiza kwamitin sulhu na MDD ya dauki matakan da suka dace, da yin kokarin kawo karshen yakin Gaza nan da nan, da sassauta yanayin jin kai, da sa kaimi ga aiwatar da shirin kafa kasashe biyu da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na dogon lokaci a yankin Gabas ta Tsakiya.(Ibrahim)