logo

HAUSA

Zirga-zirgar fasinjojin jiragen kasa ta ci gaba da karuwa a kasar Sin bayan bikin bazara

2024-02-21 16:24:48 CMG Hausa


Bayan lokacin hutun bikin bazara na bana, zirga-zirgar fasinjojin jiragen kasa domin ziyartar iyalai, da yawon shakatawa, da komawa bakin aiki da makarantu ta karu, kana bukatar zirga-zirgar fasinjoji na habaka, inda yawan fasinjoji ya ci gaba da karuwa. 

Bisa labarin da rukunin layin dogo na kasar Sin ya bayar, a jiya Talata yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 13.386, kana sufurin jiragen kasa yana cikin yanayi mai kyau. A yau Laraba kuma, an yi hasashen cewa, yawan fasinjojin da jiragen kasa suke dauka zai kai miliyan 12.1, kana za a kara yawan jiragen kasa dake daukar fasinjoji guda 1182.

Game da yanayin ruwan sama, ko dusar kankara, ko sanyi da ya shafi wurare daban daban a kasar, hukumomin jiragen kasa na wurare daban daban za su dauki matakai masu inganci don tinkarar hakan, da kuma daidaita shirin gudanar da zirga-zirgar jiragen kasa masu daukar fasinjoji, da kara karfin ba da hidimomi ga zirga-zirgar jiragen kasa, da kara sanya jiragen kasa kan hanyoyin da yanayi bai shafe su ba, ta yadda za a tabbatar da kyautatuwar zirga-zirgar fasinjoji.  (Safiyah Ma)