logo

HAUSA

Amurka da Turai za su rasa damar samun bunkasuwa mai dorewa idan suka takaita shigar da motocin Sin zuwa kasashensu

2024-02-20 20:44:57 CMG Hausa

Dangane da shirye-shiryen da Amurka da Turai suke yi na takaita shigar da motocin Sin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ta yi karin haske a wani taron manema labarai na yau da kullum Talatar nan cewa, wannan matakin zai shafi ci gabansu na dogon lokaci.

A bara, kasar Sin ta fitar da motoci miliyan 4.91 zuwa kasashen waje, wanda ya zama na daya a duniya a karon farko. Bayanan da kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin ta fitar a kwanan nan, sun nuna cewa, a watan Janairun bana, kasar Sin ta fitar da motoci dubu 443 zuwa kasashen waje, adadin da ya karu da kashi 47.4 cikin 100 kan na shekarar 2023 wanda ya ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri. A sa'i daya kuma, Amurka na tunanin yin amfani da wasu hanyoyin da ba kudin haraji ba, wajen takaita shigo da motoci masu fasahar zamani na kasar Sin da sauran sassan da ke da alaka da su. Kungiyar Tarayyar Turai ta kuma kaddamar da wani bincike kan motocin Sin masu amfani da wutar lantarki.

Mao Ning ta yi nuni da cewa, bayanan da kasar Sin ta fitar game da fitar da motoci na nuna irin ci gaban da ake samu a masana'antar kere-kere ta kasar mai inganci da ma muhimmancin kirkire-kirkire. Mao Ning ta jaddada cewa, ya kamata mu yi la'akari da muradun wasu yayin da muke kare muradun kanmu, da inganta ci gaba tare yayin neman ci gaban kanmu, samar da yanayi na kasa da kasa, mai dogaro da kasuwa, da doka don hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, ita ce alkiblar hada kai. (Zainab Zhang)